By Fatima Dayyab
NA-ALLAH YAYI AIKIN ALLAH:
A karo na biyu a bana, wani Alhajin Najeriya daga karamar hukumar Gumi ta jihar Zamfara, ya tsinci makudan kudaden Turai wato Euro har €1,75 0, kwatankwacin Nairar Najeriya Miliyan N2,,876,475 a Harami wato Masallacin Ka’aba.
Alhajin Mai suna, Muhammad Na-Allah, ya mika wadannan makudan kudade a hannun shugaban hukumar Alhazan Najeriyar, Malam Jalal Arabi, domin neman mai su.
Da yake karbar kudaden, shugaban hukumar Alhazan ta Najeriya, Malam Jalal Arabi ya fassara aikin Alhairin da Alhajin ya yi da sunansa wato Na-Allah.
Malam Jalal Arabi wanda ya ce aikin Alhaji Na-Allah ya nuna cewar akwai alamun tarbiyar da aikin hajji ke koyarwa ta shigi Alhaji Na-Allah, a tarbiyance da Dabi’ance.
Indan za a iya tunawa, a makon da ya gaba ma an samu wani Alhaji Daga jihar Jigawa da Shima ya tsinci kudaden Kasar Ingila, da na Kasar Rasha da Riyal din Saudi Arabia.